Connect with us

Labarai

Tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku ta tattauna da manyan ƴan majalisar dokokin Amurka

Published

on

Tawagar yaƙin neman zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ta fara tattaunawa da manyan jami’an majalisar dokokin Amurka kan batun sahihancin zaɓe a Najeriya.

Rahotonni sun bayyana cewa an gudanar da taron ne ta ƙafar Internet tare da jami’an na Amurka.

Haka kuma, yayin wannan ganawa, rahotonni sun ce, an tattauna zarge-zargen da ke cewa wasu na ƙoƙarin karkatar da zaɓen jama’a, tare da duba yadda tafiyar mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke gudana musamman kan batun zargin murkushe yan adawa.

Sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangarorin da abun ya shafa.

Ta cikin wani rahoto da jaridar PUNCH ta fitar, wani kamfani mai zaman kansa, ya ce zai ci gaba da fallasa duk wanda aka samu da hannu wajen maguɗin zaɓe, tare da bada shawarar ladabtarwa a kansu a ƙasashen waje, ciki har da hana su shiga Amurka da kuma daskarar da kadarorinsu.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ƙara nuna damuwa a duniya kan yadda ake gudanar da zaɓe a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!