Labarai
Kotu ta dakatar da kansiloli daga tsige mataimakin shugaban karamar hukuma a Kano
Wata babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a karamar hukumar Ungoggo ta yanke hukuncin dakatar da kansilolin karamar hukumar Rogo daga daukar duk wani mataki kan mataimakin shugaban karamar hukumar Alhaji Nasiru Dalha Rogo har sai ta kammala shari’a kan batun dakatar da shi da kansilolin su ka yi.
A cewar kotun kowa ya ci gaba da kasancewa a matsayin da yake, zuwa karshen shari’ar da ta ke saurara kan batun dakatarwar tare da tsige mataimakin shugaban karamar hukumar ta Rogo, Nasiru Dalha Rogo.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Nasiru Saminu ta dakatar da matakin da kansilolin karamar hukumar ta Rogo suka dauka har zuwa lokacin da za ta zartar da hukunci kan batun.
Kotun ta kuma bai wa wadanda ake kara, wa’adin makwanni biyu da su kare kansu daga zargin.
Haka zalika kotun ta kuma daga ci gaba da sauraran karar zuwa ranar hudu ga watan gobe na Agusta.
Tun farko dai Alhaji Nasiru Dalha ne ya shigar da karar gaban kotun yana kalubalantar dakatar da shi da kansilolin karamar hukumar su ka yi, har na tsawon watanni shida sannan daga bisani suka kuma nada wani ya maye gurbinsa.
You must be logged in to post a comment Login