Ƙetare
Kotu ta hana sakin tsohon shugaban ƙasar Afrika ta Kudu Jacub Zuma

Wata babbar kotu a kasar Afrika ta Kudu ta ƙi yarda da hukuncin da aka zartar na sakin tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma.
A ranar laraba ne kotun ta zartar da wannan hukunci da aka nemi a saki Mista Zuma saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
A watan satumbar da ya gabata ne, wata kotu ta yanke hukuncin a saki tsohon shugaban ƙasar Afrika ta Kudu saboda rashin lafiya.
Mista Jocub mai shekaru saba’in da tara a duniya an ɗaure shi tsawon watanni goma sha biyar, bisa laifin raina umarnin kotu.
You must be logged in to post a comment Login