Labaran Kano
Kotu ta saka ranar da za ta kawo karshen shari’ar tsohon sarki Muhammadu Sunusi na biyu da gwamnatin Kano
Babbar Kotun Tarayya, dake zamanta a Abuja, ta saka ranar 30 ga watan Nuwambar wannan shekara a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin karar da tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya shigar gabanta, na zargin gwamnatin jihar Kano da da take masa hakkin sa.
Mai shari’a Anwuli Chikere, ne ya tsayar da ranar a jiya bayan da lauyoyin bangarorin biyu suka amince da hakan.
Tsohon sarkin na Kano Malam Muhammadu Sunusi na biyu, ya yi karar Sufeton ‘yan sandan kasar nan da shugaban hukumar tsaro na kasa DSS Kan tsareshi da akayi ba bisa ka’ida bah.
Wanda hakan yasa yake karar su kan tauye masa hakkin sa, tare da cusguna masa a lokacin da yake tsare a hannun su.
You must be logged in to post a comment Login