Labarai
Kotu ta sanya ranar cigaba da shari’ar Winifred Oyo-Ita
Babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja karkashin jagorancin Justice Taiwo Taiwo, ta sanya ranar 20 ga watan Oktoba mai zuwa domin ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Winifred Oyo-Ita.
Mai shari’a Taiwo-Taiwo ya ce ya dage zaman ne sakamakon rashin samun cikakkun bayanai game da zaman kotun na yau, a don haka ya ga babu zabi face dage zaman shari’ar.
Ya kara da cewa kotun za ta zauna a ranakun 20 da kuma 21 na oktoban, bayan kammala hutun shekara da alkalai ke zuwa.
A ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta gurfanar da Misis Oyo-Ita da wasu makusantanta guda biyu, Ubong Effiok da kuma Garba Umar, kan zarge-zarge guda 18.
Zarge-zargen sun hada da na badakalar kudi naira miliyan 471.
You must be logged in to post a comment Login