Labarai
Kotu ta yanke wa Ike Ekweremadu, da Mai dakinsa hukuncin ɗaurin shekaru Tara
Kotu a kasar Burtaniya ta yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa, hukuncin ɗaurin shekaru Tara a gidan gyaran hali.
Kotun dai tana tuhumar su da aikata laifin yunkurin safarar sassan jikin dan Adam.
Kotun ta yanke musu hukuncin ne tare da wani likita mai shige musu gaba bayan da suka kai wani matashi Birtaniya daga jihar Lagos.
Sanatan mai shekara 60, da mai ɗakinsa Beatrice ‘yar shekara 56, sun so a cire wa matashin Koda ne da nufin dasa wa ‘yarsu mai suna Sonia ‘yar shekara 25, kamar yadda ma’auratan suka bayyana wa Kotu.
Tun da farko kotu ta samu ma’auratan da likitan mai suna Dakta Obinna Obeta, mai shekara 50, da laifin haɗa baki dashi wajen aikata laifin.
You must be logged in to post a comment Login