Labarai
Hukumar Kwastam ta tara harajin Naira Biliyan 63.78 a Kano da Jigawa

Hukumar Kwastam mai kula da shiyyar Kano da Jigawa ta sanar da cewa ta tara kuɗaɗen haraji da suka kai Naira biliyan 63.78 tsakanin watan Janairu zuwa Yunin shekarar 2026. Hukumar ta ce adadin ya fi abin da aka tara a irin wannan lokaci na shekarar 2025, lamarin da ta bayyana a matsayin ci gaba mai ƙarfafawa.
Mukaddashin Kwanturolan Hukumar Kwastam mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Usman Umar Adamu, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar hukumar da ke Kano. A cewarsa, nasarar ta samo asali ne daga sabbin tsare-tsaren da Shugaban Hukumar Kwastam na ƙasa ya ƙaddamar.
Hakazalika, hukumar ta bayyana cewa ta kwace kayayyakin da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 1.711, waɗanda aka shigo da su ƙasar ba bisa ƙa’ida ba. Daga cikin kayayyakin akwai sabbin motoci, jarkokin man gyada, kwantena, magunguna da sauran kayayyaki.
Mukaddashin Kwanturolan ya kuma bayyana cewa daga farkon watan Yuli zuwa yanzu, hukumar ta sake tara kusan Naira biliyan 3.922 a matsayin kuɗaɗen haraji, inda ya jaddada cewa za su ci gaba da ƙarfafa matakan tattara kuɗaɗen shiga tare da yaƙi da safarar kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login