Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta zauna don sauraren ƙarar Ganduje

Published

on

Yanzu haka babbar kotun jihar Kano mai lamba 4 ta zauna domin fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta shigar.

Gwamnatin jihar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

Gwamnatin jihar kano dai tana zargin Ganduje da waɗanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

Tuni dai aka girke jami’an tsaro a harabar Sakatariyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!