Labarai
Abuja: Kungiyar malamai ta NUT ta tsunduma yajin aiki

Kungiyar malamai ta kasa (NUT) reshen birnin tarayya Abuja ta fara yajin aiki a safiyar yau sakamkon gaza biyan wasu bukatunsu da ministan Abuja ya yi.
Hakan na zuwa ne bayan wani zama na musamman da kwamatin amintattun kungiyar ya zartar bayan wani taro da ya gudanar.
Kazalika kungiyar ta bukaci iyayen dalibai da su zaunar da ’ya’yansu a gida har sai an warware matsalolin.
NUT ta ce ta ɗauki matakin ne bayan wa’adin kwanaki bakwai da ta bai wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙare, ba tare da warware dukkan matsalolin su ba.
Daga cikin buƙatun malaman akwai fitar da rahoton kwamitin da aka kafa tun a shekarar 2025 da kuma aiwatar da shi da cire sharadin guraben aiki da kuma sake duba tsarin yin karin girma ga malaman.
You must be logged in to post a comment Login