Labarai
Kotun Sudan ta yanke wa jagoran RSF hukuncin ɗaurin rai da rai

Wata kotu a jihar Port Sudan, da ke ƙasar Sudan ta yanke wa jagoran RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da ”Hemedti”, hukuncin ɗaurin rai da rai.
A wata shari’a da aka yi a bayan Hemedti, wanda bai halarci kotun ba, an same shi da laifin aikata kisan ƙare dangi da laifukan yaƙi da laifukan jin ƙai da kuma hare-hare kan fararen hula.
Hukuncin kotun da aka yanke ranar Lahadi 12 ga watan Yulin 2026, shi ne mafi girma da aka yi wa jagoran na RSF tun bayan fara yaƙin a 2023.
Shari’ar ta mayar da hankali ne kisan da aka yi w gwamnan Yammacin Darfur, Khamis Abbakar, a shekarar 2023.
An zargin garkuwa da shi sannan aka kashe shi bayan da ya zargi dakarun RSF da aika kisan ƙare dangi.
Hukuncin ya kuma haɗa da wasu manyan jami’ar RSF, ciki har da ƴan’uwan Hemedti, Abdelrahim Dagalo da Algoney Dagalo, duk a bayan idonsu.
You must be logged in to post a comment Login