Labarai
Mutane 792 ne suka rasu sakamakon hare-haren yan ta’adda

Aƙalla mutane 792 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren yan ta’adda guda 882 da suka auku a faɗin kasar nan a cikin watan Yunin bana, kamar yadda rahoton kamfanin nazarin harkokin tsaro na SARI Global ya bayyana.
Rahoton ya ce, dakarun sojin kasar nan sun kuma kashe mayaƙan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya 274 a wannan lokaci.
Rahoton ya ce ƙungiyar ISWAP ta ƙara kai hare-hare a yankin Monguno da ke jihar Borno, lamarin da ya hana kai kayan agaji ga dubban mutanen da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira.
Haka kuma hare-haren sun shafi garuruwan Cross Kauwa, Baga da Kukawa.
Jaridar The Punch ta rawaito cewar rahoton na SARI Global ya ce mako na biyu na watan Yuni ne ya fi ɗaukar hankali, inda aka samu mafi yawan hare-hare da mace-mace, musamman a ranakun 8, 11, 13 da 14 ga watan.
You must be logged in to post a comment Login