Labarai
Kowa sai ya mallaki katin dan kasa kafin ya zama cikakken dan kasa – Pantami
Gwamnatin tarayya ta ce daga yanzu zai zama wajibi ga duk dan kasar nan da zai bude asusun ajiya na banki ko yin rajistar zabe ya gabatar da lambar shaidar zama dan kasa ta NIN.
Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin fasahar zamani Isa Pantami ne ya bayyana haka a Abuja lokacin da ya ke ganawa da shugabannin kungiyar masu kamfanonin wayar tarho ta kasa.
A cewar Pantami burin gwamnatin shine ganin duk wani dan kasar nan ya kasance yana da lambar shaidar zama dan kasa.
Wannan na zuwa ne a lokaci guda da kamfanonin sadarwar ke bukatar gwamnatin da ta tallafa musu wajen cike gibin jari a bangaren sadarwa da ya kai akalla naira tiriliyan goma sha biyar
You must be logged in to post a comment Login