Manyan Labarai
Hotunan bikin cikar makarantar firamaren BUK shekaru 50 da kafuwa

Jami’ar Bayero dake jihar Kanon Najeriya ta yi kira ga iyaye da gwamnatoci a Najeriya kan su rinka baiwa karatun Firamare dana Sakandare muhimmancin da ya kamata domin samar da ilimi mai nagarta a kasar nan.
Shugaban jami’ar ta Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wajen taron bikin murnar cikar makarantar Firamaren jami’ar wato Staff School shekaru hamsin da kafuwa, da tsofaffin daliban makarantar suka shirya.
You must be logged in to post a comment Login