Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Ku rika yiwa ƴaƴanku gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi kafin a ɗaura musu aure – Buba Marwa

Published

on

Shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA Burgediya janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, ya yi kira ga iyaye a ƙasar nan da su tabbata an yiwa ƴaƴansu gwajin ƙwayoyi kafin a ɗaura musu aure.

 

A cewar shugaban hukumar ta NDLEA yin hakan zai taimaka gaya wajen rage matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da ya yi ƙamari tsakanin al’ummar ƙasar nan.

 

Burgediya janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan yadda za a daƙile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da ya gudana a garin Lokoja da ke jihar Kogi.

 

Shugaban hukumar ta NDLEA ya kuma ce ko da matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan a wannan lokaci na alaƙa ne da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!