Labarai
Ku yi adalci cikin ayyukan ku – saƙon Ganduje ga alƙalai
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci rantsar da sabbin alƙalan manyan kotunan jihar Kano tare da babban sakatare guda ɗaya.
Alƙalan sun haɗa da Zuwairah Yusif, da Maryam Ahmad Sabo, Sai Hafsat Yahya Sani, da Abubakar Abdu Maiwada, da Jamilu Shehu Sulaiman, da Sunusi Ado Ma’aji sai kuma wanda aka rantsar a matsayin babban sakatare Aminu Ahmad Bahaushe.
A yayin rantsarwar da yammacin Jumu’ar nan gwamna Ganduje ya yi kira ga alƙalan da su jajirce a aikin su ba tare da sanya son rai aciki ba, domin dimokuraɗiyya ba zata ci gaba ba sai da ɓangaren shari’a.
Ya kuma yi kira ga sabon babban sakataren da ya riƙe aikin sa da muhimmancin gaske inda ya ce an tura shi ma’aikatar gidaje da sufuri ta jiha.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa kafin rantsar da alƙalan da baban sakataren gwamna Ganduje ya karɓi baƙuncin tawagar sharifai na jihar Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban sharifan Sheikh Sidi Fari.
You must be logged in to post a comment Login