Labarai
Kun san hakiman da aka sauke a Kano?
Maimartaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke hakiman garin Bichi da Dawakin Tofa da Danbatta da Minjibir da kuma Tsanyawa.
Idan zaku iya tunawa dai gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya kirkiro sabbin masarautu hudu a jihar, sai dai dattawan jihar da kuma masu nada Sarki sun kai gwamnan kara kan kirkirar masarautun.
Daya daga Hakiman Sarkin Bai Hakimin Danbatta Alhaji Mukhtar Adnan na cikin mutane hudu dake nada sarki a Kano, ya kai sama da shekara sittin da hudu a kan sarautar.
Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullam Bashir Hayatu Jantile yace ya kamata a duba shekarun Sarkin Bai da gwagwarmayarsa da kuma irin gudummuwar da ya bayar kafin zartar da hukuncin.
Bashir Jantile ya kara da cewa shi dai wannan hakimi shi ne mutun na farko da ya fara yin kwamishinan ilimi a jihar Kano, kuma yana cikin wadanda suka nemowa Najeriya ‘yancin kai lokacin mulkin Tafawa Balewa.
Sannan a matsayinsa na Sarkin Bai mai zabar sarki uku a Kano irin su marigayi sarkin Kano Inuwa da marigayi sarki Ado Bayero da sarkin yanzu Malam Muhammadu Sanusi II a cewar Jantile.
Labarai masu alaka:
Kowane Gauta: Bashir Jentile ya nemi Ganduje ya mutunta umarnin kotu kan sabbin masarautu