Labarai
Kungiyar JOHESU da AHPA sun sha alwashin tsunduma yajin aiki a fadin kasar nan
Gamayyar hadin gwiwar kungiyoyin ma’aikatan Lafiya ta JOHESU da ta AHPA ta sha alwashin tsunduma yajin aiki a fadin kasar nan, matukar gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatunsu cikin wa’adin da suka bayar.
Shugaban gamayyar kungiyar ta JOHESU Kwamared Biobelemoye Joy Josiah da Sakatariyar kungiyar Florence Ekpebor sun bayyana cewa, daukar matakin ya biyo bayan wata ganawa ta musamman ta kwanaki uku da suka yi a Abuja, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta sake nazartar tsarin gudanar da cibiyoyin lafiya na tarayya.
Haka zalika sun shaida cewa sunayen mambobin hukumomin cibiyoyin lafiyar da aka wallafa a cikin watan Disambar bara ya saba dokokin da suka samar da Asibitocin koyarwa.
Gaayyar kungiyoyin JOHESO da AHPA din sun sanar da cewa matukar gwamnatin tarayya ta gaza sanya mambobinta cikin wancan tsari na jagorantar manyan cibiyoyin lafiya na tarayya, har zuwa kwanaki 21 da bayar da wannnan sanarwa to ba shakka za su tsunduma yajin aiki.