Labarai
Gwamnatin Jigawa za ta kashe fiye da miliyan 419 don inganta kiwon lafiya

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe kuɗi naira miliyan 419.47 domin inganta ayyukan kiwon lafiya na matakin farko da kuma biyan alawus-alawus ga ma’aikatan lafiya na gaba-gaba a faɗin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, ne ya sanar da hakan bayan taron Majalissar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Dutse ranar Talata.
A cewarsa, za a fitar da naira miliyan 362.8 ga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 281 da aka tantance a ƙananan hukumomi 27 na jihar, ƙarƙashin shirin Direct Facility Financing na Asusun Basic Health Care Provision Fund.
Ya bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka wa cibiyoyin lafiya su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, su samar da magunguna masu muhimmanci, tare da inganta kula da marasa lafiya, musamman a yankunan karkara da ke fama da ƙarancin samun kulawar lafiya.
You must be logged in to post a comment Login