Coronavirus
Kungiyar kwadago ta bukaci a dau matakan Kariya na Corona
Kungiyar kwadago ta kasa NLC, reshen jihar Kano ta bukaci ma’aikata gwamnati dasu kara himma wajen daukar matakan kariya na yakar cutar Corona a fadin jiha da kasa baki daya.
Kiran na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar reshen jihar kano Kwamrade Kabiru Ado Minjibir.
Kwamrade Kabiru Ado Minjibir ya kuma bukaci al’umma dasu zauna a gidajen su, musamman ma ma’aikatan gwamnati na tsawon kwanaki goma sha hudu a wani bangare na dakile yaduwar cutar.
Labarai masu alaka.
A bi dokokin jami’an lafiya don kare yaduwar cutar Corona -Farfesa Musa Abdulkadir Tabari
Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19
Haka zalika kungiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki da ma’aikatan lafiya da na kafafen yada labarai dasu kara kaimi wajen fadakar da al’umma kan hanyoyin magance cutar mai lakabin Covid 19.
Har ila yau sanarwar ta kuma ja hankalin al’umma dasu cigaba da tsaftace muhallansu da wanke hannaye da kuma yin amfani da abun rufe fuska wato ‘FACE MASKS ‘ a matakan kiyaye kai daga kamuwa da cutar.
Sanarwar ta yabawa gwamnatin jihar Kano bisa daukar matakai daban -daban a fadin jiha a kokarin da take na dakile cutar Corona.
You must be logged in to post a comment Login