Labarai
Kungiyar likitoci ta bukaci a mayar da inshorar lafiya ta zama tilas ga yan Najeriya
Kungiyar likitoci ta Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya maida shirin Inshorar lafiya ya zama tilas ga ‘yan Najeriya.
Shugaban kungiyar ta kasa Francis Faduyile ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci ‘ya’yan kungiyar suka kai ziyarar aiki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja cewa daukar matakin na tilasta wa ‘yan Najeriya suka shiga shrin ya zama wajibi kuma hakan zai taimaka wajen tabbatar wa ‘yan Najeriyar sun sami ingantaccen kiwon lafiya.
Wanna na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawun shugaban kasa Mr, Femi Adesina ya fitar cewa idan kowa ya shiga shirin hakan zai taimaka wajen samun sauki ga masu fama da cututtuka da suka hada da cutar daji ko Kansa da Siga da dai sauran su, da yawancin ke bukatar kashe kudaden masu yawa.
Haka zalika shugaban kungiyar likitocin Francis Faduyile ya nunar cewa a yunkurin da ake yi wajen sauya fasalin shirin na NHIS kawo yanzu kudirin dokar ya tsallake karatu na 3 a zaurin majalisar yayin da zauren majalisar na 8 ke karewa kafin na 9 su karbi shahadar aiki.