Labarai
Kungiyar ma’aikatan lantarki ta janye yajin aikin data tsuduma
Kungiyar ma’aikatan dake samar da wutar lantarki ta kasa ta janye janye yajin aikin sai baba ta gani da tsunduma ajiya Laraba.
Shugaban kungiyar ta kasa Kwamarred Joe Ajaero ya tabbatar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taro da ministan lantarki Saleh Mamman a Abuja.
Joe Ajaero yace manbobin kungiyar sun damu matuka wajen shawo kan matsalar ‘ya’yan kungiyar,bayan da suka bada wa’adin kwanaki 21 da a biya musu bukatun su ammagwamnati ta gaza yin hakan.
A jiya ne dai kungiyar reshen jihar Kano ta garkame babbar sharlkwatar kamfanin KEDCO dake nan Kano, bayan da ta sanar cewa ta sami umarnin shiga yajin aiki daga uwar kungiyar ta kasa.
Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan dake Samar da wutar lantarki ta kasa shiyar arewa maso yamma kwamared Muhammad Musa, ne ya bayyana haka ya yin da yake zantawa da manema labarai a yau.
Kungiyar ma’aikatan lantarki sun garkame ofishin KEDCO
Kungiyar GREKIN ta nemi gwamnatoci da su inganta tituna
‘Yan Najeriya na fuskantar karancin abinci – kungiyar FAO
Kwamared Muhammad Musa, yace sun dauki matakin ne sakamakon Gaza biya musu bukatun su da kamfanonin da suke yiwa aiki su.
Ya kuma ce akwai ma’aikatan da suka bar aiki sama da dubu biyu wanda har ya zuwa yanzu an gaza biyan su hakkokin su na barin aiki duk da cewa sun mika korafe-korafen su ga ministan samar da wutar lantarki na kasa.