Manyan Labarai
Kungiyar manoma ta AFAN ta koka kan bada bashi na Noma
Gamayyar kungiyoyin manoma ta AFAN sun bukaci gwamnati tarayya da ta binciki ayyukan shirin baiwa manoma basuka da inshorar noma na NIRSAL.
Kungiyoyin sun bukaci hakan ne a yayin wata ganawa da manema labarai da suka gudanar a Abuja.
A wani yunkuri da sukayi don jawo hankalin gwamnati kungiyoyin sun rike alluna masu rubutu, dake kiran gwamnati ta binciki shirin kasancewar yana cike da almundahana da cutar da manoma a cewar kungiyar.
Labarai masu alaka.
Taimakon kai-da-kai shi ne mafi a’ala ga manoma – Kungiyan manoma ta Kano
An bude sabbin filayen noman rani a jami’ar Bayero
Daya daga cikin mamba na kungiyar a nan jihar Kano Malam Buhari Kura, ya ce shirin karkashin bankin kasa CBN,ya maida hankali ne wajen baiwa manoma basuka, a wani mataki na bunkasa harkokin noman su, sai dai hakan ya bar baya da kura kasancewar shirin bai riksi manoman na aini hi.
Malam Shehu Umar, daya daga cikin kungiyar masu neman tumatur ya koka akan cewar babu dan kungiyar ko mutum daya da ya samu tallafin noma daga shirin na NIRSAL a shekarun da suka gabata.
An fito da tsarin ne da hadin gwiwar ma’aikatar noma da ci gaban karkara ta gwamnatin tarayya, da nufin samawa manoma sauki da bunkasa sana’oin noma a fadin kasar nan, tare da samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login