Labarai
Kungiyar Miyyetti Allah ta bukaci shugaba Buhari ya sa a kamo wadanda ke da hannu wajen kisan
Kungiyar Fulani makiyaya ta kasa Miyyetti Allah da aka fi sani da MACBAN ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da cewa an kamo wadanda ke da hannu wajen kisan Fulani a jihohin da dama na Najeriya.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Baba Usman Ngeljarma ta ce kiran mai da Martani ne kan umarnin da shugaban kasa ya bayar kan a kamo wadanda ke da hannu wajen kashe-kashen da aka samu a jihar Benue.
Kungiyar ta kuma kara da kira ga shugaban kasa da ya tabbatar da cewa an kamo wadanda ke da hannu wajen kisan al’ummar Fulani a Mambila da Numan da kuma Kajuru tare da gurfanar da su gaban shari’a domin rayukan wadanda aka kashe a wadannan wurare na da matukar muhimmancin.
Kungiyar ta kuma yi fatan cewa za’a tabbatar da cewa wadanda za’a kamo din ainahin wadanda suka yi kisan ne, amma kuma a tabbatar an kamo wadanda suka kaddamar da hari a Mambila.
Kungiyar ta kara da cewar ta yi Allah wadai da kisan tare da tabbatar da cewa tana goyon bayan shugaban Buhari wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.