Connect with us

Labarai

Kungiyoyin ‘yan kasuwar mai sun zargi NMDPRA da nuna wariya kan lasisin shigo da fetur

Published

on

Kungiyoyin ‘yan kasuwar man fetur a Najeriya sun zargi Hukumar Kula da Harkokin Mai ta  Kasa, NMDPRA, da bai wa wasu tsirarun kamfanoni lasisin shigo da fetur, lamarin da suka ce na haifar da rashin adalci da kuma tauye gasa a kasuwar man fetur.

 

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne yayin zaman tattaunawa da Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da harkokin mai na kasa, inda kungiyoyin DAPPMAN, IPMAN da MEMAN suka gabatar da korafe-korafensu kan matsalolin da ke addabar bangarorin.

 

Sakataren zartarwa na DAPPMAN, Olufemi Adewole, ya ce kamfanoni iri daya ne aka rika bai wa lasisin shigo da fetur a zangon farko, na biyu da na uku na shekarar 2026, duk da cewa akwai wasu kamfanoni da suka cika ka’idojin yin hakan,Ya ce hakan na iya rage gasa, dakile zuba jari da kuma sabawa manufar bude kasuwar man fetur da Dokar Masana’antar Mai ta PIA ta tanada.

 

Kungiyar ta kuma ce bayanan da ta samu daga NMDPRA sun nuna cewa akalla gidajen ajiyar man fetur 72 cikin 154 da aka ba lasisi ba su gudanar da kasuwanci yadda ya kamata cikin shekara guda da ta gabata, lamarin da ya jefa su cikin matsin tattalin arziki.

 

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da harkokin mai na kasa, Ikenga Ugochinyere, ya ce kwamitin zai binciki zarge-zargen tare da gayyatar jami’an NMDPRA domin su bayyana ka’idojin da suke bi wajen bayar da lasisin shigo da fetur din.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!