Connect with us

Labarai

Kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi na Jihar Kano ya kama mutane 13

Published

on

Kwamitin Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi na Jihar Kano ya kama mutane 13 da ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyi

Kwamitin hadin gwiwa da hukumomin tsaro da aka kafa domin yaki da shan miyagun kwayoyi da safarar haramtattun kwayoyi a Jihar Kano ya fara gudanar da samamen aikinsa na farko, karkashin jagorancin Shugaban Sashen Yaki da Daba, CSP Bashir Gwadabe.

An gudanar da samamen ne da misalin karfe 5: minti 15 na yammacin jiya laraba, inda aka zagaya yankunan Sakatariyar Audu Bako, Kofar Dan’agundi, Filin Mahaha da kuma tsakiyar birnin Kano.

A yayin samamen, jami’an tsaron sun kama mutane goma sha uku da ake zargi da hannu wajen ta’ammali da miyagun kwayoyi a harabar Sakatariyar Audu Bako.

Hukumar ta ce an gudanar da aikin cikin lumana ba tare da fuskantar wata turjiya ko korafi ba.

Daya daga cikin wadanda aka kama, mai suna Muhammad Babale mai shekaru 40, wanda aka fi sani da Batte daga unguwar Zango, na cikin mawuyacin hali sakamakon maye, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

Ana sa ran za a ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargin domin daukar matakin da ya dace da su bisa doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!