Addini
Kuruciya ce ta sanya na ba da wasu fatawoyi da ake zargi na akansu a yanzu – Pantami
Ministan sadarwa da bunkasa fasahar tattalin arziki Dr. Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa kuruciya ce ta sa ya ba da wasu fatawoyi da ake zargin sa akansu a yanzu.
A cewar shehin malamin, kalaman da ya yi kan kungiyar Al Qaeda da Taliban a shekarun baya , ya yi sune bisa kuskure, lokacin yana da karancin shekaru.
A baya-bayan nan dai Pantami na fuskantar suka daga wasu al’ummar kasar nan game da kalaman da ya yi a shekarun baya, wanda ke nuna alamun yana goyon bayan kungiyar Al-Qaeda da Taliban.
Masu amfani da kafafen sada zumunta sun bukaci ministan da ya yi murabus ko kuma in ya gaza yin hakan, shugaba Buhari ya sallame shi.
Da ya ke amsa tambayoyi yayin tafsirin azumin watan Ramadan a masallacin Al-Noor da ke Abuja a jiya Asabar, Shehin Malamin ya ce, da ya girma ya kara hankali ya fuskanci illar kalaman da ya yi wanda wasun su ya yi su ne lokacin yana jami’a.
‘‘A cikin shekaru 15 da suka gabata na rika zagayawa sassa daban-daban na kasar nan ina gabatar da mukala da ke nuna adawa da ta’addanci. Na ziyarci Katsina, Gombe, Borno, Kano har zuwa Difa a Jamhuriyar Nijar ina wa’azi kan kyamatar ayyukan ‘yan ta’adda’’ inji Pantami.
‘‘Na sha kalubalantar akidar boko haram karara a bainar jama’a, a wurare da dama. Na yi rubuce-rubuce da harshen hausa, ingilishi da larabaci duk da ke sukar akidar ‘yan ta’adda’’
‘‘Ko da kalaman da na yi da ake buga misali da shi a yanzu, na yi shine saboda a lokacin ina da karancin shekaru, ina jami’a a lokacin’’.
‘‘Na fara wa’azi lokacin ina dan shekaru 13, a lokacin malamai da dama ba su san gaskiyar lamari game da al’amura da suke faruwa na kasa da kasa a sassa daban-daban na duniya ba, amma sai su rika daukar matsaya kan abin da basu da cikakken masaniya akai, sai kuma daga bisani su dawo su nemi afuwa a kai- inji Shehin malamin.
You must be logged in to post a comment Login