Labaran Kano
KUST Wudil ta karawa dalibai kudin makaranta
Majalisar zartarwa ta jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano dake Wudil ta amince da yin karin kudin makaranta ga dalibai.
Yayin zaman majalisar na yau Laraba ta amince da mayar da kudin makarantar zuwa naira dubu talatin da dari takwas N30,800 maimakon dubu ashirin da daya da dari biyar N21,500,00 da tsofaffin dalibai ke biya a baya.
Yayin da sabbin dalibai kuma za su biya naira dubu talatin da uku da dari biyar N33,500 maimakon naira dubu ashirin da uku da dari biyu N23,200 da sabbin daliban ke biya a baya.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar Sa’idu Abdullahi Nayaya ta ce daliban da ba ‘yan asalin jihar Kano ba, za su biya naira dubu arba’in da hudu da dari takwas 44,800.
Dalibai ‘yan kasashen ketare kuwa, za su biya naira dubu casa’in da shida N96,000.
Sanarwar ta kara da cewa kudin masaukin dalibai ma ya samu sauyi daga naira dubu biyar da casa’in N5,090 zuwa naira dubu goma da casa’in N10,090.
Labarai masu alaka:
You must be logged in to post a comment Login