Kiwon Lafiya
Kuyi dokar da za ta hana jami’an gwamnati zuwa asibitin ketare – Kungiyar likitoci ga majalisa
Kungiyar likitoci ta kasa masu neman kwarewar aiki ta bukaci majalisun dokokin tarayyar Najeriya da su samar da wata doka da za ta haramta wa masu rike da madafun iko zuwa asibitocin kasashen waje don kula da lafiyar su.
Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi shine ya yi wannan kiran ya yi zantawa da manema labarai a Abuja.
Wannan na zuwa ne a lokaci guda da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Lonodn da ke Ingila don kula da lafiyar sa.
‘‘Hakan zai taimaka gaya wajen tursasa jami’an gwamnati da ‘yan siyasa da sauran masu rike da madufin iko da su karkatar da akalarsu wajen kyautata bangaren lafiyar kasar nan’’
‘‘Naira biliyan dari biyar da miliyan saba’in da shida da al’ummar kasar nan ke kashewa a duk shekara wajen ganin likita a kasashen waje, matukar aka yi amfani da wadannan makudan kudade wajen kwaskwarimar asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya al’amura da dama za su kyautata’’ inji shugaban kungiyar likitocin.
You must be logged in to post a comment Login