Kaduna
Kwamishiniya mai wakiltar jihar Kaduna a Hukumar kidaya ta kasa tayi kira ga alummar jahar kaduna da su fito a kidaya su.

Kwamishiniya mai wakiltar jihar Kaduna a Hukumar kidaya ta kasa, Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi tayi kira ga alummar jahar kaduna, da su fito domin a kidaya su.
Ta yi kira ne, a lokacin da ta ziyarci karamar hukumar Sabon Gari, da ke a jahar, inda tace ta hanyar kidayar ne gwamnti za ta iya wadatar da su da ababen more rayuwa.
Ta ja hankalin jama’a game da mahimmacin yin rajista don karbar shaidar yin aure, haihuwa, saki, mutuwa da dai sauran su, wanda ake bayarwa a ofishin Hukumar a duk jihohin kasar nan.
A nasa jawabin, Shugaban karamar Hukumar Malam Jamilu Abubakar Albani ya ce, a shirye suke su bayar da dukkan goyon bayan da ake nema.
You must be logged in to post a comment Login