Labarai
Kwamitin zaman na Najeriya ya bayyana damuwa kan karuwar tashe-tashen hankula na siyasa
Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, NPC, ya bayyana damuwa kan karuwar tashe-tashen hankula na siyasa, kalaman tunzura jama’a da yaɗa labaran ƙarya gabanin zaɓen 2027.
Kwamitin ya ce ya gano take hakkin zaɓe guda 60 a faɗin kasar nan da aka yi.
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kwamatin na kasa Janar Abdussalami Abubakar mai Ritaya ya fitar.
Ya ce kashi 40 cikin ɗari na waɗannan laifuka na da alaƙa da yaɗa bayanan ƙarya da gurbatattun bayanai.
Kwamatin ya kuma ce hare-haren da aka kai kan harkokin siyasa da kadarorin gwamnati zuwa yanzu sun kai kashi 21.7 cikin ɗari, yayin da barazana da tsoratar da ’yan siyasa suka kai kashi 16.7 cikin ɗari.
Sauran sun haɗa da Daba, kalaman tunzura jama’a, takaita ’yancin faɗar albarkacin baki da sauran su.
Kwamitin ya yi kira ga rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike ba tare da nuna bambanci ba, tare da gurfanar da masu ɗaukar nauyin rikicin siyasa.
Ya kuma bukaci INEC ta tabbatar da bin dokokin yaƙin neman zaɓe, tare da yin kira ga jam’iyyu da ’yan takara su bi hanyoyin doka wajen warware rikice-rikice.
You must be logged in to post a comment Login