Connect with us

Labarai

Hukumar NDLEA ta lalata gonar da ake zargin ana noma tabar wiwi a Adamawa

Published

on

Hukumar yaƙi da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa, NDLEA, reshen Jihar Adamawa, ta ce ta lalata wata gonar da ake zargin ana noman tabar wiwi a yankin Grang Zah da ke Ƙaramar Hukumar Michika.

 

Hukumar ta kuma ce ta kwato buhuna 30 na busasshiyar tabar wiwi.

 

Jami’in yaɗa Labaran hukumar NDLEA a jihar, ASN Abner Yusha, ya ce nauyin tabar wiwin da aka kwato ya kai kilogiram 428.

 

A cewar NDLEA, ana zargin Baba Luka Lada Drang da mallakar gonar, amma har yanzu ba a kama shi ba amma ta ce tana ƙara ƙoƙarin cafke shi, yayin da kayayyakin da aka kwato ke hannunta domin ci gaba da bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!