Labarai
Kwankwaso ya bar mana bashin sama da naira biliyan 54 – Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano ta ce tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya bar mata bashin sama da naira biliyan 54, na aikin titin kilomita biyar-biyar a kananan hukumomi 44 na Kano.
Kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin Kano, game da batutuwan da suka tattauna a taron majalisar zartarwa ta Jiha.
Ya ce majalisar zartarwar ta karbi rahoton kwamitin kwararrun da suka bibiyi kwangilar gina titunan karkashin rusasshiyar ma’aikatar kasa da tsare-tsare, karkashin kulawar hukumar tsara birane ta KNUPDA, bayan ziyartar kananan hukumomi 39.
Ya kara da cewa an kwace kwangilolin kananan hukumomi 3 da suka hadar da Warawa da Ungogo da kuma Dawakin Tofa, sai kuma wani bangaren na aikin Tsanyawa da Bichi, tare da baiwa wasu kwangilar.
Haka zalika ya ce an sauya wuraren da aka bayar tun farko na kananan hukumomin Rimin Gado da Karaye da kuma Bunkure, inda kuma aka sauya aikin kananan hukumomin Dala da Nassarawa da Gwale da Municipal da kuma Tarauni zuwa wasu ayyukan na daban, a madadin kilomita biyar-biyar din.
You must be logged in to post a comment Login