Labaran Wasanni
Kylian Mbappe ya ja kunnen Cavani da ya kiyayi haduwar su
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Kylian Mbappe ya ja kunnen tsohon dan wasan kungiyar da ya koma Manchester United Edinson Cavani da ya kiyayi haduwar su.
A gobe Talata ne United za ta kaiwa PSG ziyara a cigaba da gasar Champions League da ake fafatawa a bana.
Mbappe ya ce ba zai daga wa Cavani kafa ba matukar suka hadu a wasan su na gobe.
Cavani dai ya koma Manchester United ne a matsayin kyauta bayan ficewar sa daga PSG.
You must be logged in to post a comment Login