Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kaduna ta kwato sama da hekta 500,000 na filayen Noma da yan bindiga su ka mamaye

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta kwato sama da hekta dubu dari biyar na filayen Noma da a baya ’yan bindiga suka karbe iko da su a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

 

Maiyaki ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani, cikin shekaru uku da suka gabata, ta samu nasarar kwato sama da hekta dubu dari biyar daga hannun ’yan bindiga, abin da ya ce zai taimaka wajen dawo da ayyukan noma da sauran harkokin rayuwa a yankunan da matsalar tsaro ta shafa.

 

Kwamishinan ya ce rashin tsaro na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban al’umma, inda ya bayyana cewa a baya manoma a yankunan da ’yan bindiga suka mamaye ba sa iya zuwa gonakinsu.
Ya kuma ce ayyukan ’yan bindigar sun sanya matafiya da dama daina yin amfani da hanyar Kaduna zuwa Abuja saboda fargabar hare-hare.

 

Sai dai Ahmed Maiyaki ya ce yanzu lamarin ya sauya, saboda ingantuwar tsaro a fadin Jihar Kaduna, yana mai cewa matsalar da ta sa mutane ke tsoron yin balaguro tsakanin Kaduna da Abuja ta zama tarihi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!