Connect with us

Labarai

Hukumar NRS ta musanta rahoton cewa za ta dauki sabbin ma’aikata

Published

on

Hukumar tattara Haraji ta Najeriya, NRS, ta musanta wata sanarwar daukar sabbin ma’aikata da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka wallafa da sunan tsohuwar Hukumar Tattara Haraji FIRS.

 

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yau Litinin a birnin tarayya Abuja.

 

Ta cikin sanarwar hukumar ta ce, ta samu labarin wata sanarwar da ke tallata guraben aiki a hukumar, tare da neman masu neman aikin su aika bayanansu zuwa adireshin Email.

 

A domin haka hukumar ta ce, sanarwar bogi ce, kuma ba daga ita ta ke ba, inda ta gargadi jama’a da su yi hattara ka da su fada hannun masu damfara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!