Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Wadanda suka warke daga Corona a Kano sun zarce na Abuja

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da sallamar mutane 63 da suka warke daga cutar Covid-19 a jihar.

Wannan adadi dai ya sanya adadin wadanda suka warke a Kano ya zarce na birnin tarayya Abuja.

A alkaluman hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC na ranar Litinin yace mutane 53 ne suka warke daga cutar ta Corona a birnin Abuja wanda shi ne gari na biyu da cutar ta fara bulla a kasarnan.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano sanar an shafinta na Twitter cewa zuwa ranar Litinin mutane 666 ne aka gano suna dauke da cutar a Kano.

32 daga ciki sun rasu, sai 63 da aka sallama bayan sun warke.

A ranar Litinin dinnan ne gwamnatin Kano ta tsawaita dokar kulle da zaman gida a jihar har tsawon mako guda.

Karin labarai:

Ganduje ya gana da sarakuna kan Coronavirus

Yadda cibiyar gwajin Corona ta Dangote ke aiki a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,224 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!