Labarai
Labari mai dadi : NIMC ta samar da manhaja ta wayar salula da za’a yi rijisata
Hukumar bada lambar zama dan kasa ta NIMC ta fitar da wata manhaja ta wayar salula da za a rika yin rajistar cikin sauki.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Femi Adeluli mataimaki na musamman ga ministan sadarwa na kasa, Isa Ali Ibrahim Pantami.
Sanarwar ta kuma ce yanzu haka al’ummar Najeriya na iya amfani da manhajar ta, NIMC Mobile App, a wayoyin su domin yin rijistar katin na dan kasa cikin sauki.
Manhajar dai ta samar da ingantacciyar hanya ga dukkan ‘yan Nijeriya wajen lambar sijistar katin na dan kasa cikin sauki ba tare da wahala ba, ta yadda kuma za su iya hade lambar wayar su da katin dan kasa ta cikin manhajar nan ta ke.
You must be logged in to post a comment Login