Kiwon Lafiya
Lafiyar kwakwalwa shi ne jigon rayuwar ko wane bil’adama – Likita
Lafiyar kwakwalwa ita ce jigon gudanar da rayuwar ko wane bil’adama, inda take shafar mu’amala da kuma zamantakewar rayuwa, ta hanyar shafar yanayin tunanin ‘dan adam da kuma yadda yake gudanar da rayuwarsa baki-daya.
Likitoci sun bayyana cewar lafiyar kwakwalwa tana da matukar muhimmaci ga yaro da babba, yayin da rashin kulawa da lafiyar ka iya janyo matsaloli daban-daban, da suka hadar da tsoro ko rashin nutsuwa ko kuma jirkita yanayin tunanin dan adam.
Dr Aminu Abdullahi Taura, babban likita ne a sashen kula da lafiyar kwakwalwa na asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya yi bayanin yadda ake ganewa idan mutum ya samu karancin lafiyar kwakwalwa.
Dr Aminu Taura ya kara da cewa kamata ya yi a baiwa lafiyar kwakwalwa muhimmanci, saboda rashin bayyanar illolin rashin lafiyar a jiki kan janyo hadari ga dan adam.
Bincike ya nuna cewa ko wane bil’adama yana cikin hadrin kamuwa da tabuwar lafiyar kwakwalwa, kasancewar cutar ba ta la’akari da shekaru ko jinsi ko kabila.
You must be logged in to post a comment Login