Siyasa
laifukan zabe: Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 120
Rundunar ‘yan sadan Najeriya ta ce
aka kama mutane 120 a wasu daga cikin jihohin kasar 36, sakamakon zargin su da aikata laifukan zabe, yayin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalsiun tarayya da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ACP Frank Mbah ne, ya bayyana hakan lokacin da ake hira da shi kai tsaye a wani gidan Rediyo a jihar Enugu, inda ya lura da cewa ababen fashewa talatin da takwas aka gano a wurare daban-daban yayin zaben na ranar Asabar.
A cewar ACP Mbah binciko wadannan ababen fashewar ya taimakawa jami’an ‘yan sanda kara kaimin inganta tsaro don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankalin da lumana a fadin Najeriya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan na kasa ya kuma ce an gano ababen fashwar na daga cikin abinda ya sanya ba’a fuskanci tashe-tashen bamabamai ko kuma ababen fashewar a yankunan kudu maso yamma, da kudu maso kudu, kudu maso gabas da kuma arewa ta tsaki da ke tarayyar kasar nan.
Frank Mbah ya kuma tabbatarwa da al’ummar Najeriya cewa rundunar zata kara kaimi wajen binciko masu yunkurin aikata laifukan zabe, kuma wdanda aka cafke din za’a dauki tsauraran matakai a kan su, domin hakan ya kasance izina ga masu yunkurin aikatawa.
Ya kuma ce rundunar ‘yan sandan kasar ta shirya tsaf domin tabbatar da cikakken tsaro a yayin zaben gwamnoni da na ‘yan majalsiun jihohi, kuma duk wanda aka kama da yunkurin tayar da rikici ko kuma kawo tarnaki ga ayyukan hukumar zabe, shakka babu zai fuskanci hukunci mai tsanani.