Labaran Wasanni
LALIGA – Huesca da Alaves sun sallami masu horarwar su
Kungiyar kwallon kafa ta Huesca dake buga gasar Laligar kasar Spaniya ta sallami mai horar da kungiyar, Michel Sanchez, sakamakon rashin ta buka abin azo a gani da bai yi ba, a kakar wasanni ta shekarar 2020/2021.
Huesca ita ce ta 20 kuma ta karshe a teburin gasar Laligar kasar ta Spaniya inda ta ci wasa daya cikin wasanni goma sha takwas data buga a kakar bana.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Deportivo Alaves ta sallami mai horarwar ta Pablo Machin bisa rashin ta buka a bin a zo a gani da bai yi ba a kungiyar.
Yanzu dai cikin wasanni 18 da aka buga a gasar ta Laliga kungiyar ta Alaves tana mataki na 16 ya yin da ta ci wasanni hudu a kakar bata.
Huesca dai ta yi rashin nasara a wasanni hudu cikin wasanni biyar data buga a kwana-kwanan nan.
Yanzu dai mataimakin mai horar da kungiyar ta Deportivo Alaves Javier Cabello ne zai rike kungiyar a matsayin na kwarya- kwarya kafin ta bayyana sabon mai horarwar ta.
Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan ta bayyana sallamar mai horarwar a yau.
You must be logged in to post a comment Login