Labarai
Lalurar ciwon suga ka iya ta’azzara a lokacin Azumi:- Dr Abdulkareem Muhammad
Wani kwarararran likita da ke aiki a hukumar lafiya ta duniya WHO Dakta Abdulkareem Muhammad, ya ce masu fama da lalurar ciwon Suga na cikin barazanar samun karuwarsa a wannan lokaci na azumin Ramadan.
Dakta Abdulkareem Muhammad ya bayyana hakan a zantawarsa da wakiliyar Freedom Radio Ummulkhairi Rabiu Yusuf.
Ya kuma ce, kamata ya yi masu ciwon Suga kafin su fara Azumi su nemi shawarar masana kan abubuwan da ya kamata su rika ci, da kuma yin gwaji a kan lokaci.
Dakta Abdulkareem Muhammad kenan kwarararran likita da ke aiki a hukumar lafiya ta duniya, da yayi karin haske kan yadda masu ciwon suga za su yi azumi.
Rahoton: Ummulkhairi Rabiu Yusuf
You must be logged in to post a comment Login