Addini
Limamai su rika hudubar da zata kawo hadin kai Sarkin Kano
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci hadin kan limaman juma’a da ke masarautar kan su rika gudanar da huduba da zata kawo hadin kan al’ummar musulmi.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne, lokacin da ya ke jawabi ga majalisar limaman juma’a, wadanda suka kai masa ziyarar ta’aziyya ta rasuwar tsohon shugaban majalisar limaman juma’ar Sheikh Fadalu Dan Almajiri, wanda ya rasu a kwanakin baya.
Sarkin na Kano ya ce, hadin kan limaman juma’a, shi ne hadin kan al’ummar Musulmi, wanda hakan zai taimaka gaya, wajen inganta dankon zumunci tsakanin musulmi.
Da yake jawabi sabon shugaban majalisar limaman juma’a na jihar Kano, Shiekh Nasir Adam, ya ce, suna da tabbacin samun goyon bayan masarautar Kano.
Shima a nasa jawabin, mataimakin sabon shugaban Sheikh Muhammad Sani Nassarawa, cewa ya yi, suna da yakinin samun hadin kan dukkan limaman juma’a na Kano tare da gabatar da huduba kamar yadda Manzon Allah yayi umarni.
Wakilinmu na fadar sarkin Kano Muhammad Harisu Kafar Nassarawa ya rawaito cewa, Sarkin na Kano ya kuma nada dagatai guda uku da suka hada da na Rukusawa, Muhammadu Sabi’u Yahya daga Kumbotso, da Isma’ila Usman na Tokarawa daga Nassarawa, sai kuma Musa Isah na Zangon Bare-bari daga karamar hukumar Unguggo.
You must be logged in to post a comment Login