Labarai
Limamin jumu’a a Kano yayi Allah-wadai da “Black Friday”
Babban Limamin Masallacin juma’a dake Unguwar Tukuntawa Dr. Abdullahi Jibril yayi Allah wadai da kiran sunan ranar juma’a da wasu ‘yan kasuwa keyi da suna ”BLACK FRIDAY” wanda yace hakan tamkar tsokanar Addinin Musulunci ne kuma duk wanda yayi hakan tabbas yayi koyi ne da yahudawa.
Dr. Abdallahi Jibril ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilin gidan Radio Freedom Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa bayan kammala Hudubar Sallar juma’a.
Dr. Abdallahi ya kuma kara da cewa koyarwar addinin Musulunci da sunnar Annabi (s.a.w) ta nunar cewa ranar juma’a na da matukar muhimmancin gaske a wajen duk wani Musulmi sakamakon tarin alkhairan da Allah ya sanya a cikin ranar juma’a don haka bai kamata musulmai su cigaba da yadda da sunan da ake kiran ranar ba, don kuwa hakan tamkar yin izgilanci ne akan Addinin Allah.
Babban Limamin Masallacin juma’ar Dr. Abdallah Jibril ya kuma nanata cewa ya zama wajibi musulmai suyi duba sosai akan yadda yahudawa suke bullo da sabbin hanyoyin da zasu hallakar da al’ummar musulmai domin samun tsira a wajen Allah.
Labarai masu alaka:
Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi
Maza sunfi bada muhimmanci ga sunnar karin aure –Halima Shitu