Labaran Wasanni
Liverpool ta lallasa Arsenal har gida a gasar Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tayi nasarar doke
Arsenal da ci 2-0 a gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Filin wasa na Emirates dai shi ne ya karbi bakuncin fafatawar da ta gudana a ranar Laraba 16 ga Maris din 2022.
A minti na 54 ne dan wasa Diago Jota ya fara zura kwallon farko jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Sai kuma a minti na 62 shima dan wasa Roberto Firmino ya kara kwallo ta biyu da ta tabbatarwa tawagarsa tafiya da maki uku a wasan da ya gudana.
Zuwa yanzu dai Liverpool na mataki na biyu da maki 59 bayan buga wasa 29 a kakar wasannin shekarar 2021/2022.
Inda ita kuma Arsenal ta ke a maki na 4 da maki 51 bayan buga wasanni 27.
You must be logged in to post a comment Login