Connect with us

Labarai

Jam’iyyar ADC ta Jigawa ta dakatar da mamba a kwamitin gudanarwata

Published

on

Jam’iyyar ADC a Ƙaramar Hukumar Buji ta Jihar Jigawa ta dakatar da mamba a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, Aliyu Gantsa, na tsawon watanni 12 bisa zarginsa da aikata abubuwan da suka saɓa wa muradun jam’iyyar.

Hakan na cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da shugabannin jam’iyyar suka fitar a Dutsen jihar ta Jigawa.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aiki ne daga jiya Litinin 19 ga watan Oktoban da muke ciki, inda dakatarwar zata ƙare a ranar 19 ga watan Oktoban, 2027.

 

Sanarwar, wadda shugabannin jam’iyyar na rumfar zaɓen mazabar Gantsa dake ƙaramar hukumar Buji suka sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne bayan nazarin batutuwan da suka shafi ladabtarwa, haɗin kai da bin ƙa’idojin gudanar da jam’iyyar.

 

Ta ƙara da cewa kwamitin zartarwa na jam’iyyar na mazabar Gantsa ya amince da dakatarwar a ranar 5 ga watan Oktoba, yayin da kwamitin gudanarwa na ƙaramar hukumar Buji ya amince da ita ranar 16 ga watan na Oktoban da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!