Labaran Kano
Ma’aikata sun yi barazanar shiga yajin aiki a Kano
Kungiyar kwadago a jihar Kano ta yi barazanar shiga yajin aikin gargadi na mako guda, matsawar aka gaza cimma matsaya tsakaninta da gwamnatin jihar.
An shirya zaman tattaunawa tsakanin kwamitin gwamnatin Kano da kungiyar kwadago ta jihar domin tattaunawa kan matsalolin da suka dabaibaye ma’aikata.
Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Kano, kwamared Kabiru Ado Munjibir a zantawarsa da Freedom Rediyo ya ce suna sa ran cimma matsaya da gwamnati a zaman su na ranar Litinin.
a cewarsa matsawar aka gaza cimma hakan, shakka babu zasu shiga yajin aiki na gargadi.
Kwamred Ado Minjibir ya ce kungiyar kwadago ta jihar Kano, bata da masaniya game da lokacin da aka fara ragewa ma’aikata albashinsu, ko da yake daga bisani gwamnatin ta nemi afuwarsu.
You must be logged in to post a comment Login