Connect with us

Coronavirus

Yadda mutane 3 na farko suka warke daga Corona a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce yanzu haka an sallami mutane 3 daga cikin wadanda suka kamu da cutar Covid-19 a jihar.

Babban jami’i a kwamitin yaki da cutar na jihar Kano Dakta Tijjani Hussain shi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da wakilinmu Nasir Salisu Zango.

Dakta Tijjani ya ce, sakamakon kulawa da suka baiwa masu dauke da cutar yanzu haka wadannan mutane 3 sun warke sarai kuma za su koma ga iyalansu a yau.

Har ila yau, Dakta Tijjani ya ce nan bada jimawa ba za su kara sallamar wasu marasa lafiya cikin wadanda suke samun kulawa a yanzu.

Izuwa yanzu dai mutane 397 ne suka kamu da cutar Covid-19 a Kano.

Mutane 8 daga ciki sun rasu sanadiyyar cutar.

Karin Labarai:

Yadda Likitoci 34 suka kamu da Corona a Kano

Kano: Bamu tafi yajin aiki a Kano ba -Kungiyar Likitoci

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!