Labarai
Ma’aikatan majalisun tarayya sun yi barazanar dakatar da ayyukansu a majalisar daga ranar Litinin din nan
Kungiyar ma’aikatan majalisun tarayya ta yi barazanar dakatar da ayyukan ta a majalisar daga Litinin din nan, kan hakkokin mambobinta da ba’a biya su ba tun shekarar 2019.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja dauke da sa hannun wakilan kungiyar su 5.
Ta cikin sanarwar sun ce suna bin bashin naira biliyan 3 da miliyan 1, wanda ya hada da bashin albashin naira biliyan 1 da miliyan 35 da kuma biliyan 1 miliyan 75 da aka ware don yin gyara a tsarin albashi mafi karanci.
A cewarsu, sama da ma’aikata dubu 1,300 ke bin bashin albashi, haka kuma babu wani daga cikin ma’aikatan majalisun dubu 2,345 da ya sami daidaito a mafi karancin albashi, tun lokacin da aka nada su a watan Yunin 2019.
You must be logged in to post a comment Login