Kiwon Lafiya
‘Yan Najeriya da dama na dauke da cutar Hanta – Jami’ar Jos
Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos ya ce a cikin mutane dari dake kasar nan mutun ashirin daga cikin su na dauke da ciwon hanta ba tare da sun san hakan ba.
Shugaban Asibitin koyarwa na Jami’ar ta Jos Farfesa Abraham Orkurga Malu, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi kan irin hanyoyin da mutane za su bi dan kare kansu daga kamuwa da ciwon hanta.
Farfesan ya bayyana hakan ne a wani taro wanda Asibitin Aminu Kano tare da hadin gwiwa da Jami’ar Bayero suka shirya dan karrama Farfesa Musa Muhammad Borodo game da kan mukamin da ya samu na shugabantar kwalejin horas da likitoci ta kasa, da ya samu halartar manyan likitoci da dama daga kasar nan.
Likitoci:Yawan shan Paracetamol ba bisa ka’ida ba ka iya haifar da ciwon Koda
Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam
Farfesa Abraham Orkurga Malu, ya yi kira ga al’umma da su dinga zuwa asibiti gwajin lafiyar su don tantance cewar ko suna dauke da cutar ko akasin haka dan basu shawarwarin hanyoyin matakan kariya.
A nasa jawabin a taron shugaban Asibitin Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, yace zabar Farfesa Borodo, a matsayin shugaban kwalejin horas da likitoci na kasa zai taimakawa cigaban lafiya musamman dan dakile cutar hanta a kasar nan.
Shi kuma daga banagren sa, shugaban sashen da aka karrama Farfesa Muhammad Borodo, ya sha alwashin ci gaba da horar da kwararrun likitoci a kasar nan dan inganta harkokin lafiya.
A karshe Farfesa Abraham Orkurga Malu yayi kira ga shugabannin siyasa dana addinai da kungiyoyi masu zaman kansu da dai-daikun mutane su bada gudunmowar su wajen magance yawaitar cutar.
You must be logged in to post a comment Login