Connect with us

Labarai

Mai horar da tawagar Barau FC ya ci zarafin Dan Jaridar Freedom

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barau FC, Eugene Agbabe, ya ci mutunci tare da yunkurin dukan dan Jaridar Gidan Rediyo Freedom Kano kana mamba na kungiyar marubuta labaran wasannin ta kasa SWAN reshen jihar Kano , Aminu Halilu Tudun Wada.

 

Hakan ya biyo bayan da Dan Jaridar ya Tambayi mai horar war tsarin salon amfani da ‘yan wasan sa da ya yi , da ya ce ya kamata ace mai horar war ya samu nasara da kwallaye masu yawa maimakon daya tilo.

 

Mai horar wa Eugene Agbabe, ya harzuka tare da cewar Dan Jaridar Bai San komai ba a kan kwallo Kuma ba shi da hurumin yi masa tambayar , don haka shi shashasha ne Kuma ya fuskanci daman baya kaunar sa.

 

A kokarin dai dai ta Lamarin Dan Jaridar Aminu Halilu Tudun Wada, ya cewa mai horar war ya fahimce shi ya Kuma Kwantar da hankalin sa , sai dai mai horar war ya kara harzuka inda ya yunkuro tare da kokarin kai dukka ga Dan Jaridar abinda sauran ‘yan Jaridu da sauran jami’ai a wajen yin hira da ‘yan jaridu suka rike shi, abinda ya sa Dan Jaridar ya bar wajen domin kai Zuciya nesa.

 

Aminu Halilu Tudun Wada, ya nuna rashin Jin dadin sa inda ya aike da sakon daukar mataki a matsayin kungiyar SWAN, a abinda ya kira cin zarafin sa da mai horar war ya yi a karo na biyu , bayan na farko da ya yi a baya , a wasan da kungiyar ta doke Ikorodu City.

 

A bangare daya kuma ana dakon abinda kungiyar marubuta labaran wasanni ta SWAN zata aiwatar dangane daLamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!